Bakonmu a Yau

Nijar: Mutane 40 sun mutu wasu dubu 140 sun rasa mahallansu a ambaliyar ruwan sama

Sauti 03:45
Ambaliyar Ruwa
Ambaliyar Ruwa AFP/Junior D. Kannah

A Jamhuriyar Nijar akalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu kusan dubu 140 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka sama a sassa daban daban na kasar a daminar bana.Hakazalika ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwar wani adadi na dabbobi masu tarin yawa, tare da lalata amfani gona kamar dai yadda mahukunta a kasar suka tabbatar.Lawan Magaji, shi ne ministan kula da ayyukan jinkai da kuma agajin gaggawa, ga karin bayanin da ya yi mana dangane da wannan ambaliya ta shekarar bana.