Nijar

Boko Haram ta karbi kudin fansa a Nijar

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram pmnewsnigeria

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar cewa, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun saki mahaifiya da kuma kanwar wani dan majalisar kasar da suka yi garkuwa da ita bayan an biya kudin fansa da adadinsu ya kai Naira milyan 20, kimanin cfa milyan 30 kenan.

Talla

Wannan ne dai karo na farko da ‘yan Boko Haram suka yi nasarar karbar kudin fansa kafin sakin wani a kasar ta Nijar, abin da kuma ke haifar da fargaba a tsakanin jama’a.

Sai dai masana harkokin tsaro a kasar kamar Mamman Danbuzuwa da ya zanta da sashan hausa na RFI, ya ce, mayakan na Boko Haram za su sake bullo da wata dabara don ci gaba da karbar kudin fansa a kasar.

Danbuzuwa ya gargadi tsanantar tashin hankali muddin kungiyar ta ci gaba da dabarun karbar kudin fansa.

Nijar na daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da ke fama da rikicin Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.