Nijar

Nijar ta kaddamar da gagarumin shirin rigakafin cutar Polio

Hoton wata jami'ar lafiya yayin baiwa karamar yarinya rigakafin cutar Polio.
Hoton wata jami'ar lafiya yayin baiwa karamar yarinya rigakafin cutar Polio. AFP/Getty/PIUS UTOMI EKPEI

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani sabon shirin rigakafin cutar Polio ko ‘shan inna’, inda ake sa ran yiwa akalla yara miliyan uku rigakafin, wadanda ke kasa da shekaru biyar.

Talla

Jami’ai a kasar sun ce matakin ya biyo bayan gano bullar cutar a wani yanki na Zinder dake makwabtaka da Najeriya, inda yara 6 suka kamu.

Rabi Souley babbar jami’ar dake jagorantar shirin rigakafin, ta ce sun soma aiwatar da rigakafin ne tun a ranar Alhamis din nan da ta gabata daga Zinder, Maradi, Agadez da kuma Diffa.

Gagarumin shirin rigakafin na baya bayan nan na zuwa ne shekaru akalla 12, bayanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta janye Jamhuriyar Nijar daga cikin kasashe masu fama da barkewar cutar Polio a matakin annoba.

A watan Afrilun da ya gabata, jami’an lafiya daga majalisar dinkin duniya sun yiwa sama da kananan yara miliyan 5 rigakafin Polio a kasar, ciki harda yaran dubu 42 dake sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin tafkin Chadi, inda Nijar din ke iyaka da Najeriya, Chadi da kuma Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.