Isa ga babban shafi
Nijar

Kashi 10 cikin al’ummar Nijar na bukatar agajin gaggawa - MDD

Wasu 'yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a gidan wani magidanci a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar da ya basu wurin zama.
Wasu 'yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a gidan wani magidanci a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar da ya basu wurin zama. REUTERS/Luc Gnago
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 10 cikin 100 na al’ummar Nijar, wato ‘yan kasar akalla miliyan 2 da dubu 300 na bukatar agajin gaggawa na abinci da magunguna cikin shekarar bana.

Talla

Rahoton majalisar, wanda ofishinta da ke birnin Yamai ya fitar, ya ce matsalolin tsaro, fari da kuma ambaliyar ruwan da suka lalata amfanin gona a wasu sassan kasar ta Nijar sun taka rawa wajen haifar da karancin abinci.

Majalisar dinkin duniyar ta ce mafi akasarin wadanda ke bukatar taimakon na zaune ne, a yankunan Tahoua da Tillaberi da ke kusa da Mali, wuraren da ke fuskantar hare-haren mayaka akai-akai.

Sauran masu bukatar agajin gaggawar a cewar Majalisar, suna zaune a kudu maso gabashin yankin Diffa inda ya fuskanci hare-haren Boko Haram.

Yankin na Diffa kadai na dauke da mutane sama da dubu 300, wadanda suka tserewa rikicin Boko Haram, zalika gidajen da suka basu mafaka na bukatar tallafi, kasancewar mafi akasarin magidantan ba masu karfi bane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.