Nijar

Dakarun Nijar sun hallaka mayakan Boko Haram da dama

Wasu dakarun soji a garin Bosso, da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, gaf da iyakarta da Najeriya. 06/2016.
Wasu dakarun soji a garin Bosso, da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar, gaf da iyakarta da Najeriya. 06/2016. AFP/ISSOUF SANOGO

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da mutuwar dakarun kasar 7 sakamakon wani hari da mayakan Boko Haram suka kai masu a jihar Diffa da ke kudu maso gabashin kasar.

Talla

Sanarwar da ma’aikatar cikin gidan kasar ta Nijar ta fitar, ta bayyana cewa a ranar juma’ar da ta gabata ne mayakan na Boko Haram suka afka wa wani gari mai suna Chetima Wanou inda suka hallaka dakarun kasar ta Nijar 7 tare da raunata wasu akalla 6.

Sanarwar ta ma’aikatar cikin gida ta ci gaba da cewa, dakarun gwamnati sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama sakamakon martanin da suka mayar, yayin da shaidu suka tabbatar da cewa an kwashe gawarwakin ‘yan bindiga da dama bayan da kura ta lafa.

‘Yan kungiyar ta Boko Haram sun zo ne dauke da mayan makamai a cikin ayarin motoci masu tarin yawa, kuma ko baya ga wadanda aka kashe, akwai ‘yan ta’adda da dama da jami’an tsaron kasar suka cafke.

Har ila yau an kwace motoci uku dauke da manyan makamai daga hannun ‘yan bindigar.

Jihar Diffa dai na daf ne kan iyakar Nijar da Najeriya, a wani yanki da ake kallo a matsayin babbar cibiyar ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.