Nijar

Mayakan Boko Haram sun kai sabon farmaki kan yankin Diffa

Wasu dakarun sojin Nijar yayin tunkarar garin Bosso da ke kudu maso gabashin kasar, a gaf da iyakar Najeriya.
Wasu dakarun sojin Nijar yayin tunkarar garin Bosso da ke kudu maso gabashin kasar, a gaf da iyakar Najeriya. AFP Photo/ISSOUF SANOGO

Rahotanni Daga Jamhuriyar Nijar sun ce mayakan Boko Haram sun kashe mutane 7, tare da sace mata biyu a Yankin Diffa.

Talla

Kungiyar Alternative tace mayakan sun kai harin ne daren ranar Jiya Asabar, inda suka kona kasuwa da gidaje da dama.

Rahotanni sun ce ko a ranar Alhamis, sai da mayakan na Boko Haram suka kai hari kauyen Karidi dake kusa da iyakar Najeriya, inda suka kashe mutane 8, cikin su harda mace guda.

A ranar 9 ga watan Maris, mayakan sun hallaka wasu dakarun sojin Nijar 9 a wani farmaki da suka kai musu a yankin na Diffa, kawanaki kalilan bayan da sojin na Nijar suka hallaka mayakan na Boko Haram guda 33.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.