Nijar

Mayakan Boko Haram sun sake kai hari a yankin Diffa

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai a garin Gingimi da ke jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar.

Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa.
Wasu sojojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. Reuters
Talla

Wani mazaunin yankin na Gingimi ya ce mayakan na Boko Haram sun kuma kone gidaje masu yawa, tare da jikkata kananan yara da dama.

Kamar yadda bayanai ke nunawa, da farko wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake ne suka tarwatsa kansu, kafin daga bisani wasu ‘yan bindiga su bude wuta, kan jama’a.

Garin Gingimi na arewancin yankin Diffa a gaf da Tafkin Chadi, yankin da yayi kaurin suna wajen fama da hare-haren mayakan Boko Haram akai-akai.

A ranar Alhamis ta makon da ya gabata mutane akalla 8 suka rasa rayukansu, a kauyen Karidi, yayinda mayakan na Boko Haram sukai hare-hare har kashi 4 a ranar Asabar inda suka hallaka mutane 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI