Nijar-Jamus

Nijar ta taka rawa wajen dakile bakin haure- Merkel

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou BOUREIMA HAMA / AFP

Bayan ganawa da shugabannin kasashe 5 na yankin Sahel a birnin Ouagadougou, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta isa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda ta gana da shugaban kasar Issoufou Mahamadou.

Talla

Merkel, ta ce Nijar na taka gagarumar rawa wajen hana kwarar baki daga Afrika zuwa yankin Turai, saboda haka ya zama wajibi a taimaka wa kasar don samar wa matasanta ayyukan yi a cikin gida.

Merkel wadda ta isa birnin Yamai a maracen jiya Alhamis, ta ce da hadin gwiwar kasashen Faransa da Italiya da Spain da kuma Kungiyar Turai, tuni suka fara aiwatar da ayyukan da suka taimaka wajen takaita kwararar ‘yan ci-rani da ke ratsa kasar ta Nijar.

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou, ya ce irin matakan da suke dauka ne suka sa aka samu raguwar baki da ke ratsa kasar daga dubu 15 zuwa dubu 5 ko kuma 10 a shekara.

A dayan bangare kuwa, Shugabar Gwamnatin ta Jamus ta bukaci kasashen Turai da su cimma matsaya ta bai-daya a tsakaninsu, dangane da yadda za su tunkari rikicin kasar Libya, wanda a cewarta shi ne umul’haba’isar wasu matsalolin tsaro da yankin Sahel ke fama da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI