Nijar

Dalibai sun yi zanga-zangar kyamar dakarun Turai a Nijar

Daliban Nijar na zanga-zanga a harabar Majalisar Dokokin Kasar.
Daliban Nijar na zanga-zanga a harabar Majalisar Dokokin Kasar. ActuNiger

Dubban dalibai sun gudanar da zanga-zanga a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar domin nuna adawa da girke sojin Faransa da na Amurka a wasu sansanoni da ke kasar.

Talla

Masu zanga-zangar na zargin sojojin kasashen Turai da rashin tabuka abin kirki a daidai lokacin da mayakan jihadi ke cin karansu babu babbaka, lamarin da ke haddasa asarar rayukan sojojin Nijar.

Daliban sun yi cincirindo a harabar Majalisar Dokokin Kasar, inda suka yi ta jinjina wa sojin Nijar.

Allunan da daliban suka yi ta nunawa na cewa, "kasarmu ta samu ‘yancinta tun a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 1960", abinda ke nufin cewa, kasar bata marhabin da agajin sojojin kasashen Turai a yanzu.

A cewar masu zanga-zangar, basu ga amfanin dakarun na Turai ba saboda  ‘yan ta’adda na ci gaba da hallaka sojojin Nijar akai akai.

A baya-bayan nan dai, Boko Haram ta kashe sojojin Nijar akalla 28, yayinda kuma mayakan na jihadi suka kai wani farmakin da bai yi nasara ba akan gidan yarin Koutoukale, inda ake tsare da miyagun ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.