Isa ga babban shafi
Nijar-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun halaka mutane 12 a Gueskerou

Wani yanki na Diffa a Jamhuriyar Nijar dake kan iyaka da Najeriya.
Wani yanki na Diffa a Jamhuriyar Nijar dake kan iyaka da Najeriya. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Mayakan Boko Haram sun halaka mutane 12 yayin farmakin da suka kai, kan yankin Gueskerou dake Diffa kan iyakar Jamhuriyar Nijar da Najeriya.

Talla

Wani mazaunin yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, Maharan sun farwa mazauna yankin ne cikin daren jiya Juma’a, kuma 11 daga cikin mamatan an harbe su ne da bindiga, sai dai babu Karin bayani kan ko a jikkata wasu da kuma adadinsu.

Zalika babu Karin bayani kan ko mayakan na Boko haram sun yi awon gaba da wasu mutanen, kamar yadda suka saba yi a baya.

Ko a watan Maris dai, mayakan Boko Haram sun kai farmaki kashi biyu a kan yankin na Gueskerou, inda suka halaka ‘yan sanda 7 da fararen hula 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.