Maigabatar da kara a Nijar ya bukaci kama Hama Amadou

Jagoran yan adawa jamhuriyar Nijar  Hama Amadou
Jagoran yan adawa jamhuriyar Nijar Hama Amadou RFI Hausa

Ofishin mai shigar da karar birnin yamai a jamhuriyar Nijer, ya bada sammacin tisa keyar madugun 'yan adawar kasar, kuma tsohon shugaban Majalisar dokoki, Hama Amadou, da ya koma gida daga gudun hijirar da yake yi na shekaru 3, zuwa kurkuku.

Talla

To sai dai sanarwar tsammacin, ta baiwa Hama Amadou alfarmar ci gaba da zaman makoki,don karban ta'aziyar rasuwar mahaifiyar sa, har nan da karshen mako.

Jagoran ‘yan adawar Jamhuriyar Nijar din ya koma gida bayan kwashe shekaru 3 yana gudun hijira ta kashin kansa, sakamakon tuhumar da ake masa kan aikata laifin safarar jarirai.

Kotun da ta saurari karar da aka kai shugaban Yan adawan Hama Amadou kan safarar jarirai ta yanke masa hukuncin daurin shekara guda a bayan idan sa, bayan ya fice daga kasar.

A shekarar 2016 shugaban yan adawar ya fice daga Jamhuriyar Nijar zuwa kasar Faransa, inda aka kamala shari’ar da aka masa ba tare da ya gurfana a kotu ba.

Bayan shekaru 3, Hmaa Amadou ya koma gida a cikin wani jirgin saman kasar Cote d’Ivoire da ake kira Air Ivoire, inda ya samu tarba daga Yan uwa da tarin magoya bayan sa.

Tsohon shugaban majalisar dokokin ya ziyarci kabarin mahaifiyar sa da ta rasu a watan jiya, kafin ya isa gidan sa.

Masu sa ido na cewa, ganin irin tarbar da ya samu, akwai alamun cewar Hama zai sake komawa cikin harkokin siyasa kamar yadda ya bayyana wajen wani taro watanni 6 da suak gabata a kasar Ghana da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI