Nijar

Hukumomin Nijar sun daure jagoran 'yan adawar kasar

Jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou.
Jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou. BOUREIMA HAMA / AFP

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sanar da daure shugaban Yan adawar kasar Hama Amadou a gidan yari domin kamala wa’adin watanni 8 daga daurin shekara guda da aka masa, saboda samun sa da laifin cinikin jarirai.

Talla

Rahotanni sun ce an tsare Hama ne a gidan yarin Filinge dake Yammacin Nijar domin kammala wa’adin daurin sa bayan yak ai kan sa kotu yau da safe wadda ta tasa keyar sa zuwa gidan kason.

Bayanai sun ce shugaban Yan adawan ya gana da lauyoyin sa da mashawarta daga Jam’iyar sa kafin daukar wannan mataki.

Tun a shekarar 2016 Hama Amadou ya tsallake ya bar kasar domin gudun hijira ta kashin kan sa, bai koma gida ba sai ranar alhamis din da ta gabata domin zaman makokin mahaifiyar sa.

Kotu ta samu Hama da laifi safarar jarirai daga Najeriya inda ta masa daurin shekara guda a watan Nuwambar shekarar 2015.

A zaben shugaban kasar da akayi na watan Maris, shekarar 2016, Hama Amadou ya zo na biyu duk da kasancewar sa a tsare a gidan yari.

A watan Agustan bana, Jam’iyyar sa ta Moden Lumana ta tsayar da shi takarar zaben shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI