Afrika

Sojojin 70 ne suka mutu a gumurzu da yan ta'adda suka kai Inates a Nijar

Dakarun Nijar a yankin Inates daf da kan iyaka da kasar Mali
Dakarun Nijar a yankin Inates daf da kan iyaka da kasar Mali ISSOUF SANOGO / AFP

Gumurzu da yan ta’adda suka kai Inates dake Jamhuriyar Nijar ya haddasa mutuwar sojojin kasar 70, yayin da aka kashe ‘yan ta’adda 57.Garin na Inates na daf da kan iyaka da kasar Mali,kasar dake fama da rashin tsaro .

Talla

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindiga masu tarin yawa ne wasu a cikin motoci wasu a kan babura, inda suka killace barikin sannan suka rika harba manyan makamai da rokoki babu kakkauta.

Shaidu sun ce lamarin ya yi muni ne saboda yadda wasu daga cikin rokokin suka fada kan rumbun ajiye makamai da kuma sashen ajiye man fetur da ke cikin barikin, yayin da alkaluma ke cewa ko baya ga sojoji 70 da suka mutu cikin har da babban kwamandan barikin, akwai wani adadi mai tarin yawa na sojojin da suka bata.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka fi samun asarar rayukan dakarun gwamnatin Nijar tun lokacin da kasar ta fara yaki da ‘yan ta’adda a shekara ta 2015.

Shugaban kasar Issifou Mahamadou da ke halartar taron kasa da kasa kan zaman lafiya a nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Masar, ya katse wannan ziyara don komawa gida kamar yadda fadar shugaban ta sanar.

Dakarun gwamnati sun mayar da martani tare da fatattakar maharan, yayin da aka tura karin sojoji cikin gaggawa don taimaka wa wadanda ke barikin na Inates.

Kamfanin dilancin labaren Faransa na afp na nuni cewa maharan sun kashe dakarun Nijar da dama a wannan hari, ana kuma bayyana mutuwar kwamnadan barikin Hassane Anoutab.

A ranar 1 ga watan yulin wannan shekara, ‘yan bindiga masu tarin yawa da aka bayyana cewa sun tsallako daga Mali ne, sun kai hari a wannan bariki, inda suka kashe sojoji 18 sannan 4 suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI