Nijar

Macron ya dage taron G5 sahel saboda kashe sojojin Nijar 70

Wasu daga cikin sojojin Nijar a cikin shirin ko-ta-kwana
Wasu daga cikin sojojin Nijar a cikin shirin ko-ta-kwana US Army/Richard Bumgardner

Farmakin ta’addancin da ya kashe sojojin Nijar fiye da 70, ya tilasta wa shugaban Faransa Emmanuel Macron dage zaman taron da aka shirya gudanarwa tsakaninsa da takwarorinsa na kasashen G5 Sahel domin tattaunawa kan lamurran tsaro.

Talla

A maimakon gudanar da wannan taro a makon gebe a birnin Pau da ke kudu maso yammacin Faransa, yanzu haka an dage taron har zuwa farkon shekarar badi.

Jamhuriyar Nijar na cikin kungiyar kasashen G5 wadda aka kafa a shekarar 2014 da suka hada da Burkina Faso da Mali da Mauritania da Chadi domin yaki da mayakan jihadi.

A ranar Talata ce ‘yan ta’adda suka kaddamar da harin kan sojojin na Nijar a karamin barikinsu da ke Inates a yammacin jihar Tilaberi mai iyaka da Mali, kuma kisan da suka yi wa sojojin shi ne mafi muni tun shekarar 2015.

Bayanai sun ce, maharan sun zo ne a kan babura, inda suka killace barikin sojin da misalin karfe 7 da rabi na yamma agogon Nijar, daga nan ne kuma suka kaddamar da farmaki a kansa.

Dakarun gwamnati sun mayar da martani tare da fatattakar maharan, yayin da aka tura karin sojoji cikin gaggawa don taimaka wa wadanda ke barikin na Inates.

Maharan sun kashe kwamnadan barikin na Inates Hassane Anoutab a wannan gumurzu.

Wannan sabon hari na dada nuna yadda yan ta’adda ke kokarin wargaza lamuran tsaro a kasar ta Nijar musaman kan iyakar kasar da Mali.

Idan aka yi tuni ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara, ‘yan bindiga masu tarin yawa da aka bayyana cewa sun tsallako daga Mali ne, sun kai hari a wannan bariki, inda suka kashe sojoji 18 sannan 4 suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.