Macron ya ziyarci kaburruran sojojin Nijar da aka kashe
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bayan ziyarar kwanaki biyu a Cote d’Ivoire, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yada zango a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar a marecen Lahadi, inda ya jajanta wa al’ummar kasar dangane da mutuwar sojoji 71 a harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Inates. Macron da takwaransa na Nijar, Muhammadou Issofou sun ziyarci kaburruran sojojin.
Shugabannin biyu sun ce za su gana cikin watan gobe a Faransa, don sake daura damarar fada da ayyukan ta’addanci a Sahel.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Souley Maje Rejeto.
Macron ya ziyarci kaburruran sojojin Nijar da aka kashe
Ziyarar Macron na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin al'ummar Nijar bukaci Faransa da ta gaggauta janye dakarunta na Barkhane saboda rashin tasirinsu a kasar a cewarsu, ganin yadda suka gaza dakile hare-hare da dama ciki har da wanda ya hallaka sojin na Nijar a barikin Inates.
Sai dai shugaba Macron ya jaddada cewa, sojojin na Faransa za su ci gaba da zama domin kuwa gwamnatin Nijar ce ta bukaci a girke su domin fada da ayyukan ta'addanci.
Tuni Macron ya koma gida bayan kammala ziyarsa a kasashen na Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu