Nijar

Gingimemen karfe ya rufto daga sararin samaniya a Nijar

Samfurin karfe a sararin samaniya
Samfurin karfe a sararin samaniya rt.com

Wani gingimemen karfe ya rufto daga can sararin samaniya, inda ya sauka a wani kauye da ke garin Tanut na Damagaram a Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya razana mazauna yankin .

Talla

Mazauna yankin sun ce, sun ji wani irin kara mai tsoratarwa tare da ganin walkiya jim kadan da fadowar wannan katoton karfe a kauyen Tazai.

Rahotanni sun ce, al’amarin ya faru ne a ranar 31 ga watan Disamban shekarar da muka yi bankwana da ita.

Tuni gwamnatin kasar ta aika tawagar kwararru da hukuomi da jami’an tsaro zuwa yankin domin gane wa idanunsu abin da ya faru.

Darektan Hukumar Ma’adinai ta Kasa a Damagaram , Na Allah Ousmane , ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari na al’ajabi, inda yake cewa, a halin yanzu wasu kwararru na musamman na gudanar da bincike kan wannan karfe da ya ce, yana da nauyi sosai.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren karin bayani daga bakin Na Allah Ousmane.

Muryar Ousmane kan ruftowar karfe a Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.