Nijar

Madugun 'yan adawa Hama Amadou ya koma Nijar

Jagoran ‘yan adawa a Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya koma kasar bayan share makonni biyu yana jinya a wani asibiti da ke Faransa, inda kai tsaye ya sake komawa a gidan yarin da ake tsare da shi.

Jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou.
Jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou. BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Rahotanni sun ce, bayan saukarsa a filin jiragen sama da ke Yamai, nan take jami’an tsaro suka wuce da Hama Amadou zuwa gidan yarin garin Filingue, inda ake tsare da shi kafin alkali ya ba shi izinin zuwa waje don duba lafiyar lafiyarsa.

An yanke wa Hama Amadou hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ne bayan samunsa da laifin sayo jarirai daga ketare, to sai dai tun a lokacin tsohon Firaminista kuma tsohon shugaban Majalisar Dokokin Jamhuriyar ta Nijar ya bayyana cewa ana yi masa bita-da-kullin siyasa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI