An yi jana'izar zaratan sojin Nijar da aka kashe

Wasu daga cikin sojojin Nijar
Wasu daga cikin sojojin Nijar ISSOUF SANOGO / AFP

An gudanar da jana’izar sojojin Jamhuriyar Nijar 9 da yan ta’adda suka hallaka a Ayorou da ke yankin Tillaberi kusa da iyakar Mali.

Talla

Ma’aikatar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da nasarar fatattakar daukacin maharan sakamakon harin saman da aka kai musu a yankin Ayorou mai nisar kilomita 200 a arewa maso yammacin babban birnin kasar, Niamey.

Tun a shekarar 2005 Jamhuriyar Nijar ke fuskantar matsalar ta’addanci akan iyakarta da kasashen Mali da Burkina Faso, musamman a yankunan Tillaberi da Tahoua, inda kusan mutane dubu 78 suka rasa matsuguninsu.

Tuni hukumomi a yankin Tilaberi mai fama da rikicin ta’addanci suka tsaurara matakan tsaro ta hanyar rufe kasuwanni tare da hana amfani da babura sakamakon hare-haren da kungiyoyin jihadi suka kai wa dakarun kasar tsakanin watan Disamba zuwa watan Janairun da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla sojoji 174.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.