Nijar

Coronavirus ta bulla a Nijar

Wani sashin birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Wani sashin birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. RFI/Roland Huziaker

Ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da rahoton bullar cutar murar Coronavirus a kasar.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar lafiyar ta Nijar tace mutumin da ya kamu da cutar dan kasar ne mai shekaru 36 dake aiki da wani kamfanin sufuri.

Sanarwar ta kara da cewa a baya bayan nan mutumin yayi tattaki zuwa kasashen Togo, Ghana, Ivory Coast da kuma Burkina Faso, kasashen da dukkaninsu suka bada rahoton bullar annobar tun a makon jiya.

Rahoton bullar annobar ta Coronavirus zuwa Nijar ya zo ne jim kadan bayanda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana fargabar cewar miliyoyin mutane na iya rasa rayukansu muddin aka bar cutar ta ratsa kasashe matalauta, inda ya bukaci taimakon kasashen duniya wajen ganin an magance ta.

Yayin da yake tsokaci kan yadda cutar ke yaduwa a kasashen duniya, Guterres yace muddin aka gaza wajen dakile ta har ta shiga kasashen matalauta cutar zata kashe miliyoyin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.