Nijar

Nijar ta kashe kasurgumin dan Boko Haram

Wasu dga cikin sojojin Nijar da ke yaki da 'yan ta'adda
Wasu dga cikin sojojin Nijar da ke yaki da 'yan ta'adda REUTERS/Luc Gnago

Ma’aikatar Tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da nasar kashe wani babban jigo a kungiyar Boko Haram, Ibrahim Fakoura a yayin wata arangama da ta kaure a  tsibirin Tafikin Chadi, inda mabuyar ‘yan ta’addar take.

Talla

Wata sanarwa daga ma’aikatar ta ce, zaratan dakarun da hukumomin kasar ta tura yankin Diffa sun aika da Ibrahim Fakoura da dimbim mayakansa barzahu.

Ana zargin Fakoura, wanda wani kusa ne a kungiyar ISIS ta Afrika ta yamma da hannu a munanan hare-haren da aka kaddamar a kasar da kuma satar mutane don neman kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.