Bakonmu a Yau
Ministan lafiyar Nijar kan bullar annobar Coronavirus a kasar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:22
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da samun mutumi na biyu da ya kamu da cutar coronavirus, bayan wanda aka samu ana farko a makon jiya.Ministan lafiya Dr Ilyasu Idi Mainasara yace wani dan kasar Italia aka gano yana dauke da cutar.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ministan Lafiyar kan halin da ake ciki a kasar dangane da matakan kare yaduwar annobar da ta bulla.