Nijar

Nakiya ta halaka mutane 4 a Nijar

Wasu yara a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin Diffa dake kasar Nijar.
Wasu yara a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin Diffa dake kasar Nijar. BOUREIMA HAMA / AFP

Rahotanni daga Diffa dake Jamhuriyar Nijar sun ce wasu mutane 4 sun mutu lokacin da motar da suke ciki ta taka nakiya kusa da iyakar Najeriya.

Talla

Magajin Garin Bosso, Bako Mamadou ya tabbatar da aukuwar lamarin da kuma mutuwar mutanen 4 a garin Toummour lokacin da motar dake dauke da daliban dake komawa gida bayan rufe makarantu ta taka nakiyar.

Yankin Diffa na fama da matsalar Yan book haram dake kai hare hare da kuma garkuwa da mutane.

A makon kiya ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar da kashe daya daga cikin shugabannin kungiyar boka haram Ibrahim Fakoura lokacin da dakarun kasar suka kai hari kusa da Tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.