Nijar
Mutum na 3 ya kamu da cutar Coronavirus a Nijar
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun sanar da samun mutum na 3 da ya kamu da cutar coronavirus bayan gano wata mata ‘yar kasar Brazil dake dauke da ita.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce matar ta shiga Nijar ne a ranar 16 ga wata daga Switzerland kuma tuni aka dauki matakin kula da ita.
Gwamnatin Nijar ta bayyana mayar da otel Gawai mai gadaje sama da 200 da Village Chinuwa mai gadaje sama da 100 a matsayin inda za’a killace masu dauke da cutar.
Fira ministan Briji Rafini ya ziyarci wuraren tare da likitoci domin ganin shirin da akayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu