Mutane kusan bilyan uku ne a killace a Duniya sabili da Covid 19
A yau asabar, yayinda Sakatary Majalisar Dinkin Duniya ke magana da France 24 da RFI,rahotanni na nuni cewa kimanin mutane bilyan uku ne za su kasance a killace a fadin Duniya ganin ta yada cutar Coronavirus ke ci gaba da yin barazana ga rayuwar jama’a.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Anmtonio Guterres a wata zantawa da yayi da kaffafen France 24 da Rediyo Faransa RFi ya bayyana matukar damuwar sa gani rikon sakainar kashi da gwamnatocin kasashen Afrika ke yiwa matakan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus a yankin.
Guterres ya roki manyan kasashen Duniya da su yiwa Allah sun mayar da hankali ga yankin Afrika don taimakawa wajen hana yaduwar cutar ,jami’in ya na mai cewa illar da Coronavirus za ta yi a Afrika mudin ba a dau matakan da suka dace ba zai zarce na kowace kasa,a haka ya dace a taimakawa Afrika da kayaki da suka dace, banda haka Guterres ya bayyana cewa nauyi ya rataya wuyan magabatan kasashe na ganin sun tsaya tsayin daka don yakar wannan annoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu