Gwamnatin Nijar ta daukewa talakawa biyan kudin wuta da ruwa
Wallafawa ranar:
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou, ya sanar da wasu sabbin matakai don yaki da cutar Coronavirus a kasar, matakan da suka fara aiki daga ranar 28 ga wannan wata na Maris.
Wasu daga cikin matakan da gwamnatin Nijar din ta dauka kan annobar sun hada da hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe a birnin Yamai inda a can ne cutar ta fi tsananta, tare da hana shiga ko fita daga birnin tsawon makwanni biyu daga ranar 28 ga wannan wata na Maris.
Shugaba Issoufou ya kuma bada umarnin soma farautar wadanda ake zaton cewa suna dauke da kwayar cutar a duk inda suke, domin yi masu gwaji a cibiyoyin kiwon lafiya da ke da kwarewa dangane da cutar.
Domin samar wa jama’a sauki wajen samun kayayyakin da ake amfani da su wajen tsafta da kuma kashe kwayar cutar ta Covid-19, gwamnati ta soke haraji a kan irin wadannan kayayyaki da ake shiga da su kasar daga ketare, yayin da za a dauki sabbin jami’an kiwon lafiya dubu 1 da 500 cikin gaggauwa don taimakawa wadanda ake da su cikin kasar a wannan yanayi.
Lura da yadda wannan cuta ta shafi harkokin yau da kullum da kuma na tattalin arziki kuwa, shugaban Issoufou Mahamadou, ya sanar cewa gwamnati za ta biya wa al’ummar kasar baki daya wutar lantarki da ruwan da za su yi amfani da su a watannin Afrilu da Mayun wannan shekara.
Wani sassaucin da gwamnatin kasar ta Nijar ta yi wa al’umma shi ne dakatar da karbar haraji kowane iri har sai cikin watan yuni mai zuwa, yayinda za a kaddamar da wani shirin raba wa jama’a marasa karfi abinci a matsayin kyauta, yayin da za a bullo da wani shirin sayar da abinci a kan farashi mai rahusa ga al’umma.
A daya bangare kuwa shugaban kasar ya sanar da yi wa fursunoni dubu 1 da 540 da ke tsare a gidajen yari daban daban afuwa domin rage cinkoso a gidajen kurkukun kasar.
A jimilce shugaban kasar ya ce karkashin wannan shiri, gwamnati za ta kashe ko kuma yafe kudaden da za su kai cfa biliyan 597.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu