Coronavirus ta sa an saki Hama Amadou a Nijar
Wallafawa ranar:
Jagoran ‘yan adawa a Jamhuriyar Nijar Hama Amadou, na daga cikin mutane 1,540 da shugaban kasar Issoufou Mahamadou ya yi wa afuwa, karkashin matakan da ake dauka don hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar.
Gidan rediyon gwamnatin kasar ta Nijar ya zana sunayen mutanen da aka yi wannan afuwa cikinsu kuwa har da Hama Amadou wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samun sa da laifin sayo jarirai daga kasashen ketare.
Hama Amadou ya kasance tsare a gidan yari tun ranar 19 ga watan Nuwamban da ya gabata.
Yanzu haka an tabbatar da cewa mutane 22 ne ke dauke da kwayar cutar a kasar da aka samu asarar rayukan mutane 3 yayin da ake sa-ido kan mutane 2,607 saboda yiyuwar yin alaka da wadanda suka harbu da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu