Nijar-Coronavirus

Ba za mu ci amanar 'yan Nijar ba a kan coronavirus-Gwamnati

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou. ©RFI

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da zargin cewa, tana kara yawan alkaluman  mutanen da ke kamuwa da cutar coronavirus a kasar domin samun tallafin kudade daga kasashen duniya, tana mai cewa, babu yadda za ta yi haka saboda cin amana ne.

Talla

Da dama daga cikin ‘yan kasar na ganin cewa, adadin da Ma’aikatar Kiwon Lafiyar kasar ke fitarwa a kowacce rana ya wuce misali, musamman ma idan aka yi la’akari da alkaluman wasu kasashe kamar Najeriya wadda ta fi Nijar yawan al’umma, amma adadin masu dauke da cutar a Najeriyar bai kai na Nijar ba.

Sai dai gwamnatin Nijar ta bakin Ministan Yada Labaranta Saleh Habi, ta musanta wannan zargi, tana mai cewa, babu yadda gwamnatin ta  shugaba Muhammadou Issofou ta yi irin wannan coge, domin hakan tamkar cin amana ne.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Minista Saleh Habi kan wannan batu.

Muryar Saleh Habi kan coronavirus a Nijar

A ranar Alhamis din nan, an samu karin mutane 25 da suka kamu da cutar coronavirus a Nijar din, tare da samun karin mutum daya da ya rasa rayuwarsa.

Sanarwar da Ma’aikatar Lafiya ta fitar ta ce, 21 daga cikin mutanen sabbin kamuwa, sun fito ne daga Yamai, sai 2 a jihar Dosso, yayin da a johohin Tawa da Zinder aka samu mutum guda-guda

A Yanzu dai adadin wadanda suka kamu cutar a kasar sun tashi zuwa 609, yayin da 105 suka warke, sai kuma 15 da suka rasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.