Nijar

Dakarun Nijar sun fafata da Boko Haram a Diffa

Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar a Diffa.
Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar a Diffa. ISSOUF SANOGO / AFP

Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar tace dakarunta sun yi nasarar dakile yunkurin mayakan Boko Haram na kai musu farmakin bazata, kan sansaninsu dake Diffa a Kudu maso Gabashin kasar mai iyaka da Najeriya.

Talla

Majiyar tsaron Nijar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar, da misalin karfe 11 na ranar Asabar din nan, mayakan na Boko Haram suka ketare gadar Doutchi da ta hada Najeriya da Nijar, da zummar farma sansanin sojin nata.

Majiyar ta ce, anyi kazamin dauki ba dadi na tsawon lokaci, tsakanin dakarun na Nijar da suka yi amfani da tankokin yaki, da kuma mayakan na Boko haram, wadanda daga karshen sojin suka yi nasarar korarsu, babu ko da soja guda da ya hallaka ko samun rauni yayin arrangamar.

Ko a farkon watan nan na Mayu, mayakan Boko Haram sun kashe dakarun Nijar 2 da jikkata wasu 3 a kusa da gadar ta Doutchi a yankin na Diffa, dake iyakar Najeriya da Nijar, kamar yadda ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar din ta tabbatar.

To sai dai cikin wani hoton bidiyo na farfaganda da reshen kungiyar Boko Haram mai biyayya da IS ta fitar, ya nuna wani hari da ta danganta shi da na ranar 3 ga watan Mayu kan sansanin sojin na Diffa, inda ta nuna irin makamai da wasu motoci da tace tayi nasarar kwace su a hannun sojin na Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.