Nijar

Gungun 'yan bindiga sun afkawa kauyuka 3 a yammacin Nijar

Wasu daga cikin dakarun sojin Jamhuriyar Nijar.
Wasu daga cikin dakarun sojin Jamhuriyar Nijar. AFP / Ludovic Marin

‘Yan bindiga masu yawa haye kan babura sun afkawa kauyuka uku a jihar Tillaberi dake yammacin Jamhuriyar Nijar, inda suka kashe fararen hula akalla 20.

Talla

Gwamnan jihar Tillaberi Tidjani Ibrahim Katiella, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, maharan sun kai mummunan farmakin ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.

Gwamnan yace, maharan sun fasa shaguna tare da kwashe kayayyakin abinci da kuma dabbobi kafin su nufi yankin kan iyakar kasar ta Nijar da Mali.

Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne kan garuruwan Gadabo, Zibane Koira-Zeni da kuma Zibane-Tegi, wadanda ke kan kusurwar iyakokin kasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso inda suka aikata wannan ta’asa.

An kai hare-haren ne kwana biyu bayanda gwamnatin Nijar ta tsawaita aiki da dokar ta baci a wannan yanki, tare da hana jama’a yin amfani da babura a matsayin ababan hawa.

Daga watan Disambar da ya gabata zuwa yanzu, ‘yan ta’adda sun kashe sojojin Nijar 174, tare da adadin fararen hula masu tarin yawa a cikin jihar Tillaberi, dake yammacin kasar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.