Nijar

Dakarun Nijar sun halaka mayakan Boko Haram 75 a Diffa

Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar a Diffa.
Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar a Diffa. Reuters

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar samun nasarar kashe mayakan Boko Haram akalla 75 a fafatawar da dakarun kasar suka yi da maharan a Yankin Diffa.

Talla

A wata sanarwa, ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta ce ‘yan ta’adda 25 ne suka gamu da ajalinsu a jihar Diffa da ke kudu maso gabashin kasar, sannan aka kashe karin wasu ‘yan ta’addan 50 a Najeriya, yayin wasu samame biyu da dakarun da ke yaki da ta’addanci a yankin suka kai.

A gabar kogin Komadougou mai nisan kilomita 74 yamma da jihar Diffa ne dakarun suka gwabza fada da Boko Haram, inda suka yi nasarar kwato motar soji guda da babura 4 da tarin makamai.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun zargi ‘yan ta’addan da kai harin da yayi sanadin mutuwar sojoji biyu da jikkata wasu 3 a sansaninsu da ke bayan garin Diffa a ranar 3 ga watan Mayu.

Wani bidiyo da kungiyar IS ta yammacin Afrika ta saki ya nuna yadda dimbim ‘yan ta’adda dauke da manyan makamai ke yin tururuwa zuwa wani sansanin soji, biyo bayan wani mummunan dauki ba dadi.

Jihar Diffa mai yawan al’umma dubu 200 da ke kusa da iyakar Najeriya, ta dandana kudarta a hannun ‘yan ta’adda da yawan hare-hare.

Alkalumman majalisar dinkin duniya na nuni da cewa ‘yan gudun hijira dubu 120 daga Najeriya na fakewa a yankin na Diffa, tare da wasu dubu 110 da rikici ya raba da muhallansu a Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.