Gwamnatin Nijar ta janye dokar hana jama'a zuwa wuraren Ibada
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Nijar ta janye dokar hana jama’a halartar wuraren ibada da a baya ta kafa don dakile yaduwar annobar coronavirus, dokar da ta shafe tsawon watanni biyu tana aiki.
Nijar din ta kuma soke dokar hana fita a babban birnin kasar Yamai, da ya zama wata cibiyar yaduwar annobar ta corona.
Sai dai gwamnati ta gindaya wasu sharudda da tace ya zama dole jama’a su kiyaye, idan har suna son sassaucin matakan kullen da ya soma aiki daga yau laraba ya dore.
Daga Maradi, wakilinmu Salissou Issa aiko da cikakken karin bayani cikin rahoton dake kasa…
Gwamnatin Nijar ta janye dokar hana jama'a zuwa wuraren Ibada
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu