Nijar

'Yan bindiga sun tilastawa karin 'yan Najeriya dubu 20 tserewa zuwa Nijar

Hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa dubban 'yan Najeriya tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.
Hare-haren 'yan bindiga ya tilastawa dubban 'yan Najeriya tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar. West Africa Reporters

Hukumomin Jihar Maradi dake Jamhuriyar Nijar, sun ce an samu karin ‘yan gudun hijira sama da dubu 20 daga jihohin Zamfara da Sokoto a Najeriya, da suka tsere zuwa cikin kasar saboda hare-haren ‘yan bindiga.

Talla

Hukumomin na Nijar sun ce a yanzu haka, dubban ‘yan gudun hijirar sun isa gundumar Gidan Runji, kari kan tsaffin ‘yan gudun hijira sama da dubu 30 dake cikin sansanoni biyar na Jihar.

Salisu Isa ya aiko da rahoto daga Maradi kan halin da ake ciki.

Karin 'yan gudun hijira dubu 20 sun tsere zuwa Nijar daga Najeriya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.