Nijar-Coronavirus

Masu corona 684 sun warke daga cikin jumillar 885 da suka kamu a Nijar

Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar this illustration taken on January 29, 2020.
Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar this illustration taken on January 29, 2020. REUTERS/Dado Ruvic

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ce sabbin mutane 9 aka samu dauke da cutar coronavirus a jiya, wadanda suka kunshi maza 6 da mata 3.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar tace a halin yanzu jumillar adadin wadanda suka kamu da cutar a Nijar ya kai 885 daga cikin mutane dubu 3 da 758 da aka yiwa gwaji.

Sanarwar gwamnatin tace tuni mutane 684 suka warke daga wannan cuta, yayinda 51 suka rasa rayukansu.

A jiya gwamnatin kasar ta Nijar ta bi sahun wasu kasashe wajen bude Masallatai domin gudanar da ibada, bayan shafe makwanni akalla 7, Masallatan na rufe da zummar dakile yaduwar annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.