Nijar-Boko Haram

Sojin Nijar 12 sun kwanta dama bayan halaka mayakan Boko Haram 7

Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar yayin sintiri akan iyakar kasar na Najeriya dake yankin Diffa.
Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar yayin sintiri akan iyakar kasar na Najeriya dake yankin Diffa. Reuters

Sojojin Jamhuriyar Nijar 12 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu 10 suka samu raunuka, a harin da mayakan Boko Haram suka kai wa barikin sojin Blabrine da ke daf da garin Diffa kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Talla

Sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta Nijar ta fitar, ta ce a lokacin harin dakarun kasar sun yi nasarar kashe mayakan na Boko Haram 7, kafin su fatattaki sauran zuwa cikin Najeriya.

Sansanin sojin na Blabirine na da tazarar kilomita 20 zuwa yankin arewa amso gabashin jihar Diffa a gaf da tafkin Chadi, inda iyakokin Kamaru, Chadi, Najeriya da kuma Jamhuriyar ta Nijar suka hadu.

Mayakan Boko Haram sun sha kai farmaki kan sansanin sojin na Blabrine dake yankin na Diffa dake kusa da iyakar Najeriya, inda yanzu haka ‘yan gudun hijira sama da dubu 300 daga Najeriyar da kuma Jamhuriyar ta Nijar ke tsugunne a sansanoni.

A ranar 13 ga watan Mayu, dakarun Nijar suka sabar da kashe mayakan Boko Haram 75 yayin fafatawar da suka yi a Diffa, lokacinda mayakan suka yi yunkurin kaiwa sansaninsu farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.