Najeriya-Nijar

Hare-haren 'yan bindiga sun karu a kauyukan dake iyakar Najeriya da Nijar

Wasu 'yan Najeriya da suka yi gudun hijira zuwa kauyen Garin Yahaya dake Jamhuriyar Nijar.
Wasu 'yan Najeriya da suka yi gudun hijira zuwa kauyen Garin Yahaya dake Jamhuriyar Nijar. © UNHCR/Sélim Meddeb Hamrouni

Yayinda 'yan gudun hijira daga Najeriya ke ci gaba da kwarara zuwa yankunan Nijar dake kan iyaka, mahukuntan kasar ta Nijar na fafutukar kawo karshen hare-haren 'yan bindiga da satar dabbobi da suka karu a kauyukan dake iyakokin kasashen 2.

Talla

A daidai wannan lokaci ne kuma shugabannin al’ummma ke kira ga hukumomin da su dau matakan tabbatar da zaman lafiya, saboda a yanzu al'ummar karkara na ci gaba da tara makamai na gargajiya ciki har da bindigogi don kare kai, lamarin a gab aka iya zama matsalar daukar doka a hannu.

Daga maradi wakilinmu Salisu Isa ya aiko da rahoto kan halin da ake ciki.

Hare-haren 'yan bindiga sun karu a kauyukan dake iyakar Najeriya da Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.