Coronavirus: Ministan ilimi mai zurfi na Nijar kan shirin sake bude makarantun kasar

Sauti 03:52
Gwamnatin Nijar za ta sake bude makarantun kasar bayan hutun dolen da annobar coronavirus ta tilasta musu.
Gwamnatin Nijar za ta sake bude makarantun kasar bayan hutun dolen da annobar coronavirus ta tilasta musu. Lucie au Niger

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar, sun ce ko shakka babu za a sake bude makarantun bokon kasar a ranar litinin mai zuwa bayan share kusan kwanaki 70 a rufe sakamakon annobar coronavirus.Ministan ilimi mai zurfi na kasar kuma shugaban kwamitin da ya kunshi masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a kasar Yahouza Sadissou, ya bayyanawa Abdoulkarim Ibrahim Shikal irin matakan da gwamnati ta dauka kafin sake bude makarantun.