Nijar ta shafe kwanaki 2 babu wanda ya kamu da coronavirus
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar lafiyar Jamhuriyar Nijar tace an shafe kwanaki 2 a jere, ba tare da samun koda mutum guda da ya kamu da cutar coronavirus a kasar ba.
A rahoton da ta fitar a baya bayan nan, maikatar lafiyar ta Nijar ta ce tun bayan bullar annobar cikinta, jumillar mutane dubu 4 da 571 aka yiwa gwaji, daga cikinsu kuma 955 suka kamu.
A halin yanzu kuma mutane 803 sun warke daga cutar, yayinda 64 suka mutu, abinda ke nufin masu cutar ta coronavirus 152 a yanzu haka suka rage a Jamhuriyarta Nijar.
Ma’aikatar lafiyar ta Nijar dai ba ta yi karin bayani kan maganin da take amfani da shi wajen warkar da wadanda cutar ta kama a kasar ba, sai dai a makwannin baya, Jamhuriyar ta Nijar ta bi sahun wasu kasashen Afrika wajen karbar 'Covid-Organics' wani maganin gargajiya da kasar Madagascar ta samar, da tace rigakafi ne kuma yana warkar da cutar ta coronavirus ko COVID-19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu