Nijar

Alkalan Nijar sun fara bahasi kan badakalar makamai

Sojojin Nijar da ke fada da ta'addanci sun koka kan karancin makamai
Sojojin Nijar da ke fada da ta'addanci sun koka kan karancin makamai ISSOUF SANOGO / AFP

Bayan binciken kwakwaf da aka gudanar kan badakalar kwangilar makamai ta Euro miliyan 110 a Jamhuriyar Nijar, yanzu haka alkalan kasar sun fara gudanar da nasu bahasi bayan an mika musu sakamakon binciken farko.

Talla

Tuni ‘Yan sandan Ma’aikatar Shari’a suka saurari mutanen da badakalar ta shafa tare da shigar da batun gaban kotu bisa dogaro da binciken karshe da kafofin yada labarai ke ci gaba da dogara da shi yanzu haka.

Shi dai wannan rahoto da aka fitar a ranar 29 ga watan Maris da ya gabata, ya nuna cewa, an tattauna tsakanin mahukumta da 'yan kwangilar, inda aka cimma matsaya kan mayar da kudaden kwangilolin da ba a mika ba.

Bayan bacin ran da rahoton farko na watan Fabrairu ya haifar a kasar, gwamnati ta bukaci 'yan kwangilar da su yi bayani domin samar da mafita ta ruwan sanyi.

Bayan makwanni uku kuma, aka sake neman 'yan kwangilar suka sake bayyana daya bayan daya a ofishin Ministan Tsaron.

Bisa tuhumar tafka ba dai dai ba wajen bada kwangilar, 'yan kasuwar sun karba laifin, kamar yadda wani kundin binciken da Radiyo Faransa RFI ya samu lekawa ya nunar.

A game da batun ninka kudaden kwangilar da masu binciken suka yi zargi a kai kuma, yan kwangilar sun amince da kudaden da suka karba, sai dai sun yi watsi da batun ninka kudaden da ake zarginsu da shi.

Har ila yau 'yan kwangilar sun bukaci da ayi la'akari da bayanan da suka gabatar kan lissafin kudaden da suka gabatar wanda ya sa kudin suka zama CFA biliyan 45 maimakon biliyan 76 da aka sanar da farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.