Human Right Watch ta zargi Sojin Nijar da kisan farar hula kan zargin Ta'addanci
Wallafawa ranar:
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta zargi sojojin Jamhuriyar Nijar da aikata laifuffukan yaki wajen kasha wasu mutane 2 da ake zargin cewar mayakan book haram ne a watan jiya.
Kungiyar wadda ta gudanar da bincike kan wasu hotunan da akayi ta yadawa ta kafar sada zumunta wanda ke nuna yadda motar yakin sojin Nijar ke markade mutanen biyu ta ce hukumomin kasar sun tabbatar da afkuwar lamarin.
Jonathan Pedneault, jami’in kungiyar Human Rights Watch ya ce faifan bidiyon ya nuna karara yadda jami’an sojin ke harbi kuma suna bi ta kan mutanen da mota.
A ranar 13 ga watan Mayu, ma’aikatar tsaron Nijar ta ce sojojin ta sun kashe 'yan ta’adda 25 a yankin Diffa da wasu abokan gaba kusan 50 a yankin Tafkin Chadi a wasu hare hare da suka kaddamar.
A ranar 3 ga watan Mayu mayakan boko haram sun sanar da kashe sojojin Nijar guda 2 a cigaba da hare haren da suka kai musu jifa jifa.
Jamhuriyar Nijar ta yi asarar sojoji da dama a yakin da take da yan ta’adda a Yankin Diffa da kuma iaykar Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu