Niger

Masu safarar makamai sun kashe junansu a Agadez

Yankin Agadez ya yi kaurin suna tun bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Gaddafi
Yankin Agadez ya yi kaurin suna tun bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Libya, Moammar Gaddafi Jakarta Globe

Rahotanni daga Agadez da ke Jamhuriyar Nijar sun ce, mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon artabun da aka yi tsakanin wasu tsageru masu safarar makamai da kwayoyi a kusa da kan iyakar kasar da Libya. 

Talla

Yankin Agadez mai makwabtaka da kasashen Algeria da Libya da kuma Nijar ya yi kaurin suna wajen aikata laifuka tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Moammar Ghaddafi ta Libya.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya rawaito cewa,  kungiyoyin tsagerun sun yi artabun ne  tsakanin ranakun Alhamis da Juma’ar da suka gabata, kuma mutane da dama sun mutu.

Wani jami’in yankin Agadez ya ce, mambobin daya daga cikin kungiyoyin ne suka yi wa takwarorinsu kwanton-bauna, a kokarinsu na mamaye haramtacciyar harkar safarar makamai da kwayoyi a  yankin.

Wata majiya ta ce, mutanen da aka kashe sun kai 17 daga bangarorin biyu.

Rundunar Sojin Amurka da ke kula da Afrika na kai hare-hare kan 'yan ta’adda da masu safarar makamai a wannan yankin lokaci zuwa lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI