Ra'ayoyin masu sauraro kan rashin baiwa 'yan Nijar mazauna ketare damar samun wakilci a Majalisa

Sauti 15:42
Wata mata tsaye a layin masu shirin kada kuri'a a Yamai ba babban birnin Jamhuriyar Nijar yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, 21/2/2016.
Wata mata tsaye a layin masu shirin kada kuri'a a Yamai ba babban birnin Jamhuriyar Nijar yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu, 21/2/2016. Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar, ta ce ba za ta iya gudanar da zabe domin bai wa ‘yan kasar dake zaune a kasashen ketare damar samun wakilci a Majalisar dokokin kasar ba, sannan kuma ba za ta iya gudanar da zaben kananan hukumomi ba duk da cewa wa’adinsu ya kawo ya kawo karshe.A baya dai cikin watanni masu zuwa aka tsara gudanar da sabbin zabuka a kasar ta Nijar, sai dai hukumar zabe ta ce ba ta da lokacin yi wa masu kada kuri’u rijista a kasashen ketare, matakin da tuni ya samu amincewar kotun tsarin mulkin kasar. Wannan shi ne batun da muka baiwa masu sauraro damar tattaunawa akai.