Nijar

Nijar na bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci daga Faransa

A yau Litinin 3 ga watan Agusta, Jamhuriyar Nijar na gudanar da bukukuwan cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Baya ga batun tsaro, cutar coronavirus da kuma yaki da gurgusowar hamada, a jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar cikin daren jiya ,shugaban kasar Issoufou Mahamadou ya jaddada ranar 13 ga watan Disamba a matsayin ranar zaben kananan hukumomi, yayin da za a yi zaben shugaban kasa na ‘yan Majalisar Dokoki a ranar 27 ga watan na Disamba.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoton wakilinmu Salissou Issa daga Maradi.

Jamhuriyar Nijar ta kai ga samun ‘yancin kai ne bayan share tsawon shekaru bangarori biyu masu bambancin ra’ayi a fagen siyasar kasar wato Sawaba karkashin jagorancin Djibo Bakary da kuma RDA karkashin jagorancin Diori Hamani na hamayya da juna, inda daga karshe turawan suka mika mulkin a hannun Diori Hamani.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren takaitaccen tarihin yadda Nijar ta samu 'yancin kanta daga bakin Maman Abdoulaye a zantawarsa da wakilinmu Ibrahim Malam Tchilo.

A wannan Litinin shugaban kasar Issoufou Mahamadou na gudanar da ziyara a garin Agadez da ke arewacin kasar domin jagorantar bukukuwan murnar zagayowar ranar ta ‘yancin-kai.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI