Nijar

MDD ta rufe sansanonin 'yan gudun hijira 2 a Nijar

Aisha Moussa daga Najeriya tare da yaranta 2 a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya a zagayen tafkin Chadi
Aisha Moussa daga Najeriya tare da yaranta 2 a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya a zagayen tafkin Chadi © UNHCR/Aristophane Ngargoune

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da rufe wasu sansanonin Yan gudun hijira guda biyu a Jamhuriyar Nijar dake dauke da duban baki da suka tserewa rikicin dake gudana a kasar Mali.

Talla

Hukumar kula da Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace an dauki matakin rufe sansanonin Yan gudun hijirar guda biyu dake Tillaberi dake kusa da iyakar Mali ne bayan amincewa da matakin a ganawar da suka yi da hukumomin Jamhuriyar Nijar.

Majalisar tace gwamnatin Nijar ta bayyana cigaba da amfani da matsugunan guda biyu a Tabarey Barey da Mangaize dake dauke da Yan gudun hijira 15,000 daga Mali ba shi zai haifar da maslaha ba.

Jami’in Hukumar a Nijar, Benoit Moreno yace tuni aka kwashe Yan gudun hijirar zuwa Ayorou dake Yankin Ouallam, yayin da yayi alkawarin cewar Hukumar zata taimaka musu wajen ganin sun zauna lafiya da mazauna Yankin, kafin a mayar da su gida.

Tuni aka mika matsugunan dake Tabarey Barey da Mangaize ga gwamnatin Jamhuriyar Nijar kamar yadda ma’aikatan cikin gidan kasar ta tabbatar, yayin da yace za’a ginawa Yan gudun hijirar sabbin gidaje domin sajewa cikin al’umma.

Jami’in yace kwashe Yan gudun hijirar zai taimaka musu wajen kare su daga haren haren Yan ta’adda, yayin da mazauna Yankin zasu samu taimako a bangaren ilimi da kula da lafiya da kuma samun abinci daga Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI