Nijar-Agadez

Rahoto kan yawaitar fadowar jiragen Amurka marasa matuki da ke sintiri a Nijar

Wani samfurin jirgi marar matuki a sararin samaniya.
Wani samfurin jirgi marar matuki a sararin samaniya. ©Fabrice COFFRINI / AFP

Rundunar sojin Amruka mai yaki da kungiyoyin tsageru da na 'yan ta’adda a yankin Sahel na amfani da jiragen sama marasa matuka, don gudanar da sintiri ko tara bayanan. Sai dai wasu daga cikin jiragen da ta ke amfani da su na fuskantar hatsurra tare da tarwatse a yankunan da jama’a ke rayuwa.Daga farkon wannan shekara zuwa yau, akalla irin wadannan kananan jirage marasa matuka uku ne mallakin Amurka suka rikito, kuma na baya-bayan nan ya faru ne a cikin wannan wata na agusta a yankin Agadez. Ga karin bayani daga wakilinmu na Agadez Umar Sani.

Talla

Rahoto kan yawaitar fadowar jiragen Amurka marasa matuki da ke sintiri a Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.