Sojinmu ba su kashe fararen hula 71 ba-Nijar

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou. SIMON MAINA / AFP

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da zargin da masu bincike na kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar CNDH suka fitar da ke zargin sojojin kasar da kashe fararen hula 71 a jihar Tillaberi da ke yammacin kasar iyaka da Mali.

Talla

Ministan tsaron kasar ta Nijar Issoufou Katambe ya ce wannan zargi ne kawai, domin kuwa sojojin kasar ba su taba kashe fararen hula ba a wannan yanki.

"Sau da dama na sha fitowa a kafafen yada labarai na kasa da kasa domin musanta wannan zargi, saboda sojojin Nijar ba su taba aikata irin wannan kisa musamman ma a kan fararen hula ba, sojojinmu mutane ne da ke cikakkiyar kwarewa akan aikinsu." inji Katambe

A ganin ka waye ya aikata wannan kisa?

Yanzu sai dai a jira a gani, amma ina tabbatar maka cewa ba sojoji ba ne, za mu ci gaba da bai wa sojoji da sauran jami’an tsaronmu goyon baya a yakin da suke yi dare da rana da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifufuka a kan iyakokinmu.

Ko watakila an kaddamar da bincike na shari’a dangane da wannan lamari?

Ni ban sani ba, amma dai na karbi rahoton Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa wato CNDH, daga nan kuma na mika shi ga bangaren shari’a wanda shi ne ke da kwarewa, yanzu alhaki ya rataya ga wuyan ma’aikatar shari’a domin mika binciken ga wadanda suka cancanta. Ita dai hukumar CNDH ta fadi abin da ta fada, mu kuma mun bayyana abin da muka sani, saboda haka sai a jira shari’a ta yi aikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.