Zaben - Nijar

Kotun fasalta tsarin mulki a Nijar ta yi watsi da takarar Hama Amadou

Madugun Adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou
Madugun Adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou AFP

Kotun Fasalta kundin Tsarin Mulki a Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da takarar Madugun jam’iyyun adawar kasar Hama Amadou dake neman shugabancin kasar a zaben dake tafe a ranar 27 ga watan Disamba.

Talla

Da yake yanke hukuncin shugan Kotun tsarin mulkin Bouba Mahamane ya ce, Hama Amadou dake takara karkashin jam’iyyar adawa ta Moden Lumana bai cancanci tsayawa takara ba, saboda hukuncin daurin shekara daya a gidan kaso dake kansa.

To sai dai kotun ta amince da takarar Mohamed Bazoum dake neman shugabancin kasar karkashin jam’iyyar PNDS tarayya mai mulkin kasar, da ake zargi ba cikekken dan Nijar bane.

Madugun adawar Hama Amadou wanda ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar na shekarar 2016, ya fuskanci daurin shakara daya a gidan kaso saboda samunsa da laifin cinikin jarirai a 2017.

Sai dai ya samu ahuwar shugaban kasa Mohamadou Issofou dangane da laifin da ya alakanta shi da siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.