Nijar
Tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou ya rasu
Wallafawa ranar:
Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Tandja Mamadou wanda ya mulki kasar daga 1999 zuwa 2010 ya rasu a yammacin wannan Talatar a birnin Yamai yana da shekaru 82.
Talla
Fadar shugaban kasar Nijar ce ta sanar da mutuwarsa ta kafafen yada labaran kasar.
Kodayake sanarwar ba ta yi bayani ba game da musabbabin rauswar tsohon shugaban kasar.
Tuni gwmnatin kasar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a duk fadin kasar domin alhinin rashin tsohon shugaban na Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu