Nijar

Tarihin marigayi Tandja Mamadou na Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou wanda ya yi ban-kwana da duniya a ranar Talata yana da shekaru 82.

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar, marigayi Mamadou Tandja
Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar, marigayi Mamadou Tandja AFP
Talla

An haifi Tanja Mamadu a 1938 a garin Maïné-Soroa da ke jihar Diffa a kudancin Jamhuriyar Nijar.

Mamadou wanda tsohon soja ne mai mukamin Laftanar Kanar, na daga cikin 'yan Majalisar Zartarwa ta Sojin da suka kifar da gwamnatin farar hula ta Jori Hamani a 1974 karkashin jagorancin Janar Saini Kunce.

Marigayin ya rike mukamai da dama da suka hada da na ministoci, yayin da ya zama jakadan Nijar a tarayyar Najeriya lokacin mulkin Janar Ali Saibu.

Tanja Mamadu ya kwabe kakin soja saboda zuwan siyasar dimokuradiya a 1990, inda ya tsunduma cikin siyasa a matsayin shugaban Jam’iyar MNSD Nasara, jam’iyyar da ta kai shi kan karagar shugabancin Jamhuriyar Nijar a cikin watan Nuwamban 1999.

An sake zaben sa a wani wa’adi na 2 a watan Disamban 2004, yayin da a karshen wa’adinsa, ya shirya zaben raba gardama a 2009 inda ya bukaci karin wa’adin shekaru 3. Amma wannan mataki ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya a ciki da wajen kasar, lamarin da ya sa daya daga cikin yaransa mai kula da rundunar da ke rike manyan makaman soja, wato Kwamanda Salu Jibbo, jagorantar yi masa juyin mulki.

Ana dai danganta Mamadu a matsayin daya daga cikin 'yan mazan jiya masu kishin Nijar da al’ummarta, wanda kuma ya yi fice wajen yin fito na fito da kamfanin hakar karfen Uranium na Areva na kasar Faransa wajen tilasta masa sauya yarjeniyoyin da ya kulla da kasar na sama da shekaru 40 da ke hana Nijar amfana da ma’adaninta.

Wannan jajircewa ta kishin kasa da Mamadou ya nuna na daya daga cikin abubuwan da suka kara haifar masa da farin jini a tsakanin al’ummar kasar ta Nijar da ke yi masa kallon jarumi mai tausaya wa talakawa.

Tanja ya rasu a ranar Talata 24 ga watan Nuwamban 2020 kuma ya bar mata 2 da yaya maza da mata da jikoki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI