Nijar

Nijar zata kara yawan dakarun ta dake yaki da ta'addanci zuwa dubu 50

Sojojin Nijar masu sintiri kan iyakar kasar
Sojojin Nijar masu sintiri kan iyakar kasar US Army/Richard Bumgardner

Jamhuriyar Nijar na shirin kara yawan sojojin ta dake yaki da yan ta’adda daga 25,000 zuwa 50,000 a cikin shekaru 5 masu zuwa.

Talla

Ministan tsaron kasar Issofou Katambe ya bayyana haka a zauren Majalisar dokoki lokacin da yake kare shirin gwamnatin kasar.

Katambe yace rundunar sojin na bukatar akalla sojoji 100,000 zuwa 150,000 domin ganin sun tsare kasar, amma daga wannan lokaci zasu fara shirin kara yawan dakarun zuwa 50,000 nan da shekaru 5 masu zuwa.

Jamhuriyar Nijar na fama da matsalolin Yan ta’adda da suka hada da boko haram da kuma mayakan Mali dake kaiwa kasar hare hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.