Nijar

'Yan Nijar fiye da miliyan 2 na neman tallafin dala miliyan 523 - MDD

Majalisar dinkin duniya na neman dala miliyan 500 don tallafawa 'yan Nijar sama da miliyan biyu.
Majalisar dinkin duniya na neman dala miliyan 500 don tallafawa 'yan Nijar sama da miliyan biyu. UNHCR

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci taimakon gaggawa daga masu bada agaji domin taimakawa ‘yan Nijar sama da miliyan biyu dake fama da matsalar karancin abinci da ambaliyar ruwa da kuma hare-haren ‘yan bindiga.

Talla

David Carden, jami’in kungiyar agaji ta Majalisar da ya ziyarci Nijar, yace suna bukatar akalla Dala miliyan 523 domin taimakawa mutane miliyan 2 da dubu 100.

Jami’in yace Nijar na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da na jinkai da matsalar tsaro da kuma tashe tashen hankulan da Yan bindigar ke haifarwa wajen kai hari kan fararen hula abinda ya haifar da talauci a cikin jama’a.

Carden yace annobar korona ta dada jefa al’ummar kasar cikin mummunan yanayi inda suke bukatar taimako sosai, yayin da yaran dake tsakanin watanni 6 zuwa shekaru 5 a duniya da yawan su ya kai 457,200 ke fama da tamowa.

Jami’in yace ziyarar da ya kai kasar ta bashi damar ganewa idan sa halin da irin wadannan mutane ke ciki, yayin da kuma ya ziyarci Ouallam dake arewacin birnin Yammai inda Yan bindiga suka kasha fararen hula 100a kauyuka guda 2 ranar 2 ga watan Janairun da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI